Za a iya cewa a cikin jam’iyyun adawa 17 an kasu gida biyu tsakanin masu mara baya ga APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Wannan hargowa ta kin amincewa da sakamakon zaben da bukatar a soke shi daga PDP da mukarrabai ya zo karshe cak kamar an dauke ruwa bayan ficewar wakilin PDP Dino Melaye, na Leba Umar Ibrahim da sauran su.
A duk lokacin da a ka kammala baiyana sakamakon wata jiha shugaban hukumar zaben Mahmood Yakubu kan tambaya ko akwai mai tambaya ko wani korafi sai ka ji shiru da hakan ya nuna duk sauran jam’iyyun da su ka zauna sun gamsu kuma ba sa bukatar sai lalle an nuna sakamakon da na’urar BVAS ta tattara, na kan takarda ya wadatar da su.
Shugaban jam’iyyat ACCORD da ke wakiltar jam’iyyar sa a zauren Muhammad Lawan Nalado ya ce ba su ga wani abun tada jijiyar wuya kan sakamakon ba.
Shi kuma daya daga wakilan APC Aminu Saleh Jaji ya ce ‘yan adawar na shure-shuren faduwa zabe ne ya sa su neman birkita zauren.
Zuwa yanzu an baiayna sakamakon zabe daga jihohi 14 cikin jihohi 36 inda Bola Tinubu na APC ya fi yawan kuri’a a jihohi 6, Atiku Abubakar na PDP ya yi zarra a jihohi 5 inda Leba ta Peter Obi ke kan gaba a jihohi 3.
Shugaban hukumar zaben wanda ya yi alkawarin duba korafin da a ka yi, ya dage cigaba da baiyana sakamakon zuwa talatar nan da karfe 11 na safe agogon Najeriya.
Saurari rahoton: