- By Hadiza Kyari
Dan takarar jam'iyya mai mulki a Najeriya Bola Tinubu ne kan gaba a kidayar kuri'un bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, kamar yadda wani sakamakon wucin gadi na kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna a jihohi 20 daga cikin 36 na kasar a ranar Litinin, sai dai jam'iyyun adawa sun fice daga wurin kirga kuri'un suna zargin an yi magudi.
Kididdigar sakamakon zaben na wucin gadi na hukumar zaben ya nuna Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ne a kan gaba da kuri’u 39.7% ko miliyan 5.4 da aka kirga, yayin da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’u 32.2% ko miliyan 4.4.
Peter Obi na karamar jam’iyyar nan ta Labour ne na uku da kusan kashi 16.3% wato kusan miliyan 2.2.
Zaben dai na cike da matsaloli na kayan aiki da na’ura wanda ya sa a wurare da dama aka kasa shigar da sakamakon zabe kai tsaye daga kowace rumfar zabe zuwa shafukanta na intanet, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi alkawarin yi domin tabbatar da gaskiya.
Babu wani abin da doka ta tanada don yin hakan, amma rashin cika alkawarin da hukumar zaben ta yi, ya sa aka tattara sakamakon da hannu a cikin unguwanni da cibiyoyin kidayar kananan hukumomi kamar yadda aka yi a zabukan baya.
“Rashin ingantattun tsare-tsare na INEC a matakai masu muhimmanci da kuma ingantacciyar hanyar sadarwar jama’a ya rage amincewa da tsarin,” in ji tawagar sa-ido ta Tarayyar Turai a cikin wata sanarwa.
Shi ma shugaban tawagar sa idon na Commonwealth Thabo Mbeki ya soki INEC kan gazawarta wajen loda sakamakon zaben a shafinta.
Ya zuwa karfe 1700 agogon GMT a ranar Litinin, INEC ta fitar da sakamakon zabe daga rumfunan zabe 66,167 kacal daga cikin jimillar 178,846, kamar yadda shafin yanar gizonta ya nuna.
“Mun dauki cikakken alhakin matsalolin tare da yin nadama kan matsalolin da suka haifar da damuwa ga ‘yan takara, jam’iyyun siyasa da kuma masu zabe,” in ji hukumar a cikin wata sanarwa.
Jam’iyyun adawa dai ba su gamsu ba, duk da haka.
“An yi wuruwuru a tsarin zaben … kuma kwata kwata mun nesanta kanmu daga tsarin,” a cewar shugaban yakin neman zaben Atiku na jam'iyyar PDP Melaye Dino, a cibiyar tattara sakamakon zabe na hukumar INEC da ke Abuja. Ita ma jam’iyyar Labour ta Obi ta soki tsarin.
Obi ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyya mai mulki inda ya lashe cibiyar kasuwancin Najeriya na Legas.
Sai dai nasarar da aka samu a jihar Legas - da kuri'u 582,454 yayin da Tinubu ya samu kuri'u 572,606 - ya kasance wani babban kwarin gwiwa ga Obi, wanda zabensa ya kalubalanci 'yan takara daga jam’iyya biyu da suka dade suna yin garambawul a karagar mulki tun bayan kawo karshen mulkin soja a 1999.
Kamfen din Obi ya dauki hankulan kanun labarai tare da yin amfani da shafukan sada zumunta da kuma mayar da hankali kan matasa da masu kada kuri’a na birane da suka gaji da matasloliln cin hanci da rashawa da rashin tsaro.
Kafin ka zama shugaban kasa, dan takara na bukatar ya samu kuri'u fiye da kowane dan takara sannan kuma ya samu kashi daya bisa hudu na kuri'un a akalla jihohi 24.
An dai samu rahotannin tashe-tashen hankula da tursasawa, ko da yake ba a kai ga yawan wanda aka fuskanta a zabukan da suka gabata ba.
A jihar Kano da ke arewacin kasar, 'yan sanda sun ce wata kungiya ta kai hari ofishin yakin neman zaben karamar jam'iyyar adawa tare da cinna wa ginin wuta da kashe mutane biyu.
‘Yan sanda sun ce sun kashe daya daga cikin maharan tare da cafke mutane hudu da ake zargi.