Najeriya Itace Kasa Ta Biyar Dake Da Yawan ‘Yan Wasa A Waje

Brazil Soccer WCup Iran Nigeria

Wani rahoto da aka fitar na nunin Najeriya itace kasa ta biyar dake da yawan ‘yan wasa dake taka leda a waje a duniya, wadda ke bayan kasashe kamar su Brazil da Argentina da Faransa da kuma Serbia. A cewar rahotan wata kungiya mai sa ido kan harkar kwallon kafa CIES tace, Najeriyar dai itace kasa da tafi kowacce kasa a Afirka yawan ‘yan wasan da suka buga tamaula a waje, suna da ‘yan wasa 596 dake wasa a kasashen duniya.

Sauran kasashe da aka ambata cikin rahotan sun hada da Senegal mai ‘yan wasa wadda ta zo ta goma da ‘yan wasa 377, sai Cote d’voire ta 11 mai ‘yan wasa 370, da Kamaru a matsayin ta goma sha biyu da ‘yan wasa 366, da Ghana a matsayin 13 da ‘yan wasa 365. Baki ‘daya kwararrun ‘yan wasan dake bugawa a yanzu wanda jimlarsu ta kai 18,660 sun fito ne daga kasashe194.

Kasar Brazil wadda ta zamanto zakaran duniya da ta lashe kofin duniya har sau biyar, itace ke jagorantar kowacce kasa da yawan ‘yan wasanta dake buga kwallo a waje, kamar yadda rahotan yace tana da ‘yan wasa har 1,784 dake wasa a wajen kasar.

Argentina wadda tazo ta biyu bayan Brazil da yawan ‘yan wasa 929, sai Faransa da ta biyo baya da yawan ‘yan wasa 758. Wadannan kasashe uku sun ‘dauki kashi 20 cikin ‘dari na ‘yan wasan dake tamaula a waje.

Kasashe 15 dake da yawan kararrun ‘yan wasa dake bugawa a waje, da akwai kasashen turai 6 da kasashe biyar daga Afirka da kuma hudu daga nahiyar Amurka.