Najeriya: Dattawan Arewa Sun Yi Tur Da Batun Raba ‘Kasa

Sanata Mustapha Bukar Madawakin Daura, mai wakiltar Katsina ta Arewa.

Wasu ‘yan Majalisar Dattawa daga shiyar Arewa, sunyi tur da wa’adin da kungiyoyin matasan arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo na su tattara nasu-ya-nasu su bar shiyyar a cikin watanni uku.

Da suke mayar da martani kan wannan batu Dattawan sun nuna cewa wannna kiraye-kiraye da ya fara fitowa daga shiyyar kudu maso gabas, ba abune da zai haifar da ‘da mai ido ba, domin yana iya kawo rashin jituwa mai karfin gaske a kasar.

Madawakin Daura, Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar Katsina ta arewa, ya ce kamata yayi ace duk abin da ake yi a zauna akan tebur tsakanin manyan arewa da matasa domin samar da mafita. Haka ne yasa aka kirkiro Majalisar Zartarwa ta gwamnoni da shugaban ‘kasa.

Sanata Bukar, ya ja hankalin jami’an tsaro da su san matakin da zasu ‘dauka, haka zalika gwamnoni da wakilan tarayya da Majalisu su zauna su samar da mafita ga wannan batu.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Mai wakilatar jihar Kano ta Kudu.

Shima Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, daga jihar Kano ta Kudu, yayi tsokaci kan batun inda yayi nuna kan cewa zama tare shine mafi a’ala. Domin kuwa dukkan mutanen Najeriya na bukatar junansu.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Dattawan Arewa Sun Yi Tur Da Batun Raba ‘Kasa - 2'45"