Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da takwaransa na kasar China ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Beijing, don musayar kudin da suka kai dala biliyan biyu da rabi, dake daidai da kudin China Yuan biliyan 16, wanda kuma yake daidai da Naira biliyan 875.
Yarjejeniyar dai ta kunshi samun wadatattun Yuan a bankunan Najeriya don ‘yan kasuwa su rika odar kayan China cikin sauki. Haka nan daga can kasar China ma ‘yan kasuwa masu sayen ma’adanai daga Najeriya su sami wadatar takardar Naira.
Masanin tattalin arziki Usha’u Aliyu, ya ce lamarin na maraba ne idan an dauke Amurka daga ciki, ganin cewa kasuwancin Najeriya yafi karfi a China ganin yadda ‘yan kasuwar Najeriya suke samo kayansu daga yanki Asia.
Sai dai Usha’u yayi kuma gargadin cewa dole ne abi a hankali kasancewar ba kasar China kadai Najeriya ke huldar kasuwanci ba a duniya.
A hangen masanin raya masana’antu Abubakar Ali, baya ga ma’adanai da China ke siya daga Najeriya akwai bukatar Najeriya ma ta shiga ke wasu kayayyaki don samun cikakkiyar fa’ida.
Najeriya dai na da tasiri a Afirka ta yawan jama’a da ma’adanai, sai dai kamfanoni da yawa sun zama gidan gizo-gizo.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5