Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Harvard Ta Gayyaci Indimi Domin Ya Musu Lacca


Mohammed Indimi
Mohammed Indimi

Babbar Jami'ar nan ta Harvard a Amurka ta gayyaci hamshakin dan kasuwa Mohammed Indimi domin ya yi wa dalibansu lacca a makarantar yau alhamis.

To ko mene ne makasudi wannan gayyatar?

"Wallahi 'yan makarantar ne kawai suka hango ni a Najeriya cewa ga wani can bai yi karatun boko ba kuma yana tafiyar da harkokinsa daidai kuma ya samu ci gaba saboda haka a gayyato ni a ji bayanin daga bakina." inji Indimin.

Dan kasuwan ya bayyana mamakin wannan gayyatar a cewarsa, "ya za a yi wani dan kauye daga Maiduguri ya samu wannan karramawar?"

Ya bayyana mana cewa a shirye ya ke ya amsa duk tambayoyin da daliban za su yi masa tare da basu lacca ganin yadda suke kallonsa a matsayin wanda yayi fice duk da rashin ilimin boko.

Saurari cikakkiyar hirarmu da shi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG