A karon farko shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa bayan shekaru uku da zama shugaban kasa.
Gwamnan jihar Badaru Abubakar ya ce baya ga bude wasu ayyuka da jihar ta kammala, shugaban zai kuma kaddamar da shirin bada kudaden akwati da gwamnatin jihar ta kirkiro.
A cewar gwamnan ziyarar zata basu damar godewa shugaban bisa ga abubuwan da ya yiwa mutanen Jigawa soboda jihar na cikin jihohin da suka mori shirin nan na N-Power. Akwai kuma shirin ciyar da yaran makaranta wanda gwamnan ya ce ya kawo taimako ainun.
Akwai ayyukan tituna da na madatsun ruwa da gwamnatin tarayya ke yi a jihar. Gwamnan ya ce duk wadannan abun godiya ne.
Ziyarar shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar ta amincewa gawmnan ya yi tazarce a zaben 2019. ‘Yan majalisar sun gamsu da irin ayyukan da suak ce gwamnan ya yi, saboda haka suka goyi bayansa domin ya cancanta ya ci gaba da mulki, kamar yadda Onarebul Idris Barau shugaban majalisar dokokin jihar.
To sai dai Onarebul Nasiru Garba Dantiye tsohon dan majalisar tarayya kuma dan majalisar dattawan APC yace duk da amincewar da majalisa tayi na cewa gwamnan ya zarce, basu isa su yi doka a kai ba domin a jam’iyyar APC dole sai an yi zaben share fage. Ko menene ma dai sai an koma kan talakawan jihar.
Ga rahoton Mahmud brahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum