Aminu Balele Kurfi da ake kira Dan Arewa da ke cikin tawagar Najeriya zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, ya zanta da sashen Hausa akan wasan da Najeriya za ta yi yau da Argentina.
Yace gwamnatin Najeriya ta basu goyon baya ta kuma ba ‘yan wasa da masu horas dasu duk abun da suke bukata.
A saboda haka, yace suna neman addu’ar kowane dan Najeriya saboda an dade ana muhawara akan buga kwallo tsakanin Najeriya da Argentina.
A bangaren Argentina akwai wasu manyan ‘yan kwalo wajen su biyar da ba zasu ci gaba da wasa ba bayan gasar ta wannan shekara saboda haka wajibi ne su nuna wa duniya cewa da sauransu. Ya ce duk abun da ‘yan kwallon Argentina suka sa a gaba babu wanda ya fi kwallon da zasu buga yau. Zasu so su kare mutuncinsu da na kasarsu.
A bangaren Najeriya, kuwa Dan Arewa yace Allah ya basu sa’a saboda sun yadda nasara daga wurin Ubangiji take zuwa. Saboda haka yau ya kamata ‘yan Najeriya su nuna irin son da suke yiwa kasar ta yin addu’a. Idan Najeriya ta ci ko tayi kunnen doki da Argentina zata wuce zagaye na gaba
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5