Tauraron Ronaldo na haskakawa yayin da Messi ke fadi tashi a Gasar cin Kofin Duniya ta 2018. Shin Tauraron Ronaldo zai ci gaba da haskakawa yayin da Messi zai ci gaba da fadi tashi a Gasar cin Kofin Duniya ta 2018?
Wasan karshe na gasar FIFA na cin Kofin Duniya 2018
Bayan karin lokaci sau biyu, Croatia ta lallasa Ingila ta tsallake zuwa wasan karshe na cin kofin duniya.
Wannan shi ne karo na uku, da **Faransa** ke zuwa zagayen karshe a gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Belgium a filin wasa na St. Petersburg da ke Rasha.
A bugun daga kai sai mai tsaron gida ya kawo karshen sa ran cin gasar kofin duniyar kasar Rasha. Croatia ta samu nasarar zuwa zagayen kusa da karshe.
Ingila ta kara fadada damarta ta samun nasara a gasar cin kofin duniya, bayan da ta doke Colombia a bugun fanareti a zagayen ‘yan 16. Sakamakon Karshe Ingila 1 (Ta ci Fanareti 4) Colombia 1 (Ta ci Fanareti 3)
Brazil ta shiga zagayen kusa da na gab da na karshe so bakwai a jere a gasar cin kofin duniya bayan da ta doke Mexico. Sakamakon Karshe: Brazil 2-0 Mexico
Bayan da aka tafi hutun rabin lokaci ba tare da an ci kwallo ba, Japan ta zira kwallon farko, daga baya kuma Belgium ta zaburo ta doke ta, lamarin da ya ba ta damar zuwa zagayen kusa da na gab da na karshe. Sakamakon karshe: Japan 2-3 Belgium
Colombia ta samu wucewa zuwa karo na gaba, yayin da Senegal ta fice daga wasannin cin Kofin Duniya na 2018.
Argentina ta shiga zagaye na gaba, yayin da Najeriya ta gaza yin kunnen doki aka kuma cire ta daga gasar.
A karawa da za’a yi Talatan nan tsakanin 'yan wasan Najeriya da Argentina, akwai akalla ‘yan wasan kwallon Argentina guda biyar da suka manyanta, wadanda da wuya su dawo gasar shekaru hudu masu zuwa saboda haka za su yi duk iyakacin kokarinsu su kare mutuncinsu na ganin sun samu nasara.
Domin Kari