Ministar Sadiya Umar Faruk ta bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin a birnin tarayya Abuja,da ya kunshi masu sa ido dubu 5 da zasu kasance cikin al’umma da zasu rika gudanar da aikin bada tallafin zamantakewa na social investment.
Wannan ya biyo bayan horarwa na makwanni 2 a matakin kasa karkashin kwamitin sa ido da tantance aikin tallafi da ma’aikatar ayyukan jinkai ta kafa domin samar da tsarin aiki da tattara bayanai saboda yin bita kan aikin da aka sa a gaba.
Ministar ayyukan jinkai, Sadiya Umar Faruk, dai ta bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 13 ne ke cin gajiyar shirin bada tallafin zamantakewa na social investment a jihohin kasar 36 da ma birnin tarayya Abuja a yanzu, lamarin da ake cigaba ta kai ruwa rana a kai inda wasu ‘yan kasar ke cewa ba a ganin aikin tallafin a kasa.
Ma’aikatar ayyukan jinkai za ta gudanar da shirin ne tare da hadin guiwar hukumomin yaki da cin hancı da rashawa na EFCC da ICPC don kula da shirin, Mallam Yushau Aliyu ya ce.
Minista, Sadiya Umar Faruk dai ta ce, ma’aikatar ayyukan jinkai zata tabbatar da cewa, ’yan sa ido masu zaman kasu zasu ci gaba da samun horo da sanar da su jadawalin ayyukan su don sauke nauyin aikin da ya rataya a wuyansu da bada gudunmuwa don cimma nasara a aikin da shugaba Muhammadu Buhari ya sa gaba na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.
Saurari rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5