Najeriya: An Gudanar Da Taron Hukumar 'Yan Sanda Ta Kasa Da Kasa

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya

A lokacin da aka bude taron rundunar 'yan sandan Duniya wato INTERPOL, a Abuja, jami'an tsaron sun tattauna batun 'yan Najeriyan nan 77 da aka samu da hannu a wajen damfarar makudan kudade a Amurka.

Rundunar 'yan sanda ta duniya ta ce ta gano aika-aika irin ta ta'addanci da safarar kwaya da mutane, da ma damfara ta yanar gizo na daga cikin sabbin matsalolin tsaro da tashin hankali a kasashe.

Wakilin babban sakataren rundunar K.G. Meslin Abeh, ya Jaddada cewa hukumar 'yan sandan ta kasa da kasa za ta sa ido don tabbatar da an dakile wannan matsala.

taron dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ta bankado wani gagarumin damfara da wasu yan Najeriya 77 suka tafka a kasar.

Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya ce galibin 'yan Najeriya ba mutanen banza bane, don haka suna goyon bayan a hukunta su domin ya zama darasi ga wasu ma.

Itama hukumar EFCC ta ce ta za ta taimakawa hukumar FBI ta Amutka wajen binciken da yakai ga bankado wannan aika aika.

A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.