Duk da cewa ba a samu yadda ake so ba sosai ta fannin ci gaba, 'yan kasar na ganin ba a makara ba wajen samar da kyakkyawan shugabanci da kai kasar ga ci gaba muddin za a yi koyi da magabata.
Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kai a shekarar 1960, jagororinta a wancan lokacin sun nuna kishi da kokarin ganin sun mayar da ita tamkar wata kasa a nahiyar Turai, sai dai wannan kudurin na su ya hadu da cikas sanadiyar juyin mulki na farko da sojoji suka yi ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966.
Farfesa Abubakar Abdullahi na sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usman Danfodiyo, na ganin cewa wannan juyin mulkin shi ne mafarin duk wata matsala da Najeriya ta samu kanta a ciki a lokacin.
Amma wani abin sha'awa shi ne yadda shugabanni a jamhuriya ta farko suka dukufa wajen ayyukan bunkasa kasa ba tare da sun ciyo bashi ba.
Dakta Tukur Mukhtar, na sashen nazarin tarihi a Jami'ar Usman Danfodiyo, shi ma ya ce har yanzu jama'ar Najeriya na amfana da ayykan da magabatan suka samar.
Masana na ganin cewa in da shugabannin da Najeriya ta samu daga baya sun yi koyi da na farko da tuni labarin da ake da shi yanzu na rashin ci gaba ya sauya, kamar yadda farfesa Abubakar Abdullahi ya bayyana.
Najeriya da ke bin tafarkin dimokradiyya yanzu bayan shekaru kimanin 63 da samun 'yancin kai, tana dab da gudanar da babban zabe a watan Fabarairu. Wasu 'yan kasar da yawa na ganin da ‘yan siyasa zasu yi koyi da halayen shugabannin jamhuriya ta farko da za a samu bunkasar kasar.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5