NAJERIYA:Abdurrasheed Bawa Ya Zama Sabon Shugaban EFCC

Abdulrasheed Bawa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da nadin Abdurrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC yau Laraba, bayan zaman sa’oi biyu ta na nazarin bukatar da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar na neman a gaggauta amincewa da nadin shi.

Da yake jagorantar zaman, shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan ya yi kira ga majalisa ta duba bukatar da shugaban kasar ya gabatar na neman a amince da zaben Abdurrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar, bisa tsarin dokar aikin hukumar na 2003 sashe na 2 sakin layi na 3.

Bayan shugaba Buhari ya gabatar da sunan Abdurrasheed Bawa ga majalisa domin rike wannan mukamin, wadansu suka fara korafin cewa, bai kamata a bashi wannan mukamin ba bisa zargin cewa, shi kansa hukumar EFCC ta taba gayyatarsa domin yin bayani a kan sayar da manyan motoci 240 da hukumar ta kwace ga mukarrabansa, zargin da hukumar EFCC ta karyata.

Abdurrasheed Bawa, wanda ya fara aiki da hukumar EFCC a shekara ta 2005, shi ne shugaban hukumar EFCC na 5. Ya gaji Ibrahim Magu wanda har zuwa lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shi a watan Yuli 2020, ya ke matsayin riko domin kasa samun amincewar majalisa.

Sabon Shugaban Hukumar EFCC Ta Najeriya Bai Ba Da Kunya Ba

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Shugaban Hukumar EFCC Ta Najeriya Bai Ba Da Kunya Ba