A hirar su da wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, Janar Manaja mai kula da sadarwa na hukumar Abdulhamid Umar Umaisha ya kara haske akai, yace wannan mataki na da alaka da matsalar tsaro.
Wannan mataki dai na zuwa ne daidai lokacin da Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ta jaddada bukatar mallakar katin zama dan kasa a shiyyar Arewa Maso Gabas.
Hukumar NIMCI tace bada lambar zai taimaka wajen inganta matsalar tsaro, kuma hakan zai taimaka wajen tantance yan kasa, da na bakin haure. Hukumar ta nuna rashin Jin dadinta da yadda, hatta wasu yan kasashen waje kanbi haramtacciyar hanya wajen mallakar katin.
Galibin 'yan Najeriya dai basu sami lambar zama dan kasa ba, al'amari da hukumar NIMCI tace bai rasa nasaba da irin dimbin matsalolin da take fama dasu. Dalilin da yasa ake shirye shiryen shigo da karin wasu hukumomin gwamnati wajen bayar da lambar ga Jama'a.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5