Kamfanonin jirgin fasinja tara da na dakon kaya hudu ne su ka mika bukatar hidima ga alhazan Najeriya domin aikin Hajjin shekarar 2024. Shugaban NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi, ya kaddamar kwamitoci 2 masu wakilai 32 domin tantancewa da su.
Jalal Arabi ya ce duk abin da a ke so a yi nasara to tabbas sai an fara shiri da wuri, domin tsadar farashin canjin dala ya zama kalubalen da a ke fafutukar daukar matakai don tabbatar da rangwame da walwalar maniyatan.
Sakataren hukumar kuma mukaddashin shugaban kwamitocin biyu Dakta Abdullahi Rabi’u Kontagora, ya ja hankalin wakilan kwamitocin da suyi aiki tsakani da Allah “Don tabbatar da duk kamfanin da a ka baiwa aikin yana da kayan aiki da muradin kare ran maniyata.”
Daraktan kamfanin Max Air Dikko Dahiru Mangal, ya ce a shirye su ke su tunkari kwamitin tantancewar, "Mu na da ingantattun kayan aiki don gudanar da aikin."
Malam Ahmad Bashir Bulma na kamfanin dakon kaya na hukumar jiragen Najeriya da ke Legas, ya ce wannan ba shi ne karo farko da su ke kula da jigilar kayan alhazai ba, "Mu na da dukkan takardun da a ke bukata don haka mu ke maraba da wannan tantancewa."
Wannan ya dai biyo bayan matsayar da hukumomin Saudiyya da hukumar alhazan Najeriya su ka cimma, na amincewa da kara yawan kamfanonin jirgin yawo da za su shiga hidimar jigilar alhazai zuwa guda 40.
Your browser doesn’t support HTML5