A yau Alhamis, Rafeal Nadal ya sanar da cewar zai yi ritaya daga wasan kwallon tennis bayan kammala wasan karshe na gasar cin kofin Davis, inda zai kawo karshen sana’ar da ta bashi damar samun kambin Grand Slam sau 22.
“Zan yi ritaya daga wasan kwallon Tennis. A zahiri al’amura sun yi tsanani a ‘yan shekarun baya-bayan nan, musammanmma shekaru 2 da suka gabata,” inji Nadal a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.
“Hakika wannan shawara ce mai wahalar yankewa, wacce ke daukar tsawon lokaci kafin a yanke. saidai a rayuwa duk abinda yayi farko ta zai yi karshe.”
An hada Nadal da Carlos Alcaraz a cikin tawagar kasar Sifaniya a yayin da yake kokarin karkare kawo karshen sana’ar tasa da samun nasara a gasar cin kofin Davis karo na 5 da zata gudana a Malaga a wata mai kamawa.
Nadal ya samu mutunci a idon duniya tare da zama gwarzon da ake koyi da shi, da kuma yin gogayya da zaratan ‘yan wasan tennis irin su Roger Federer da Novak Djokovic.