Frances Tiafoe ya fitar da Rafael Nadal a gasar Tennis ta US Open inda ya doke shi da ci 6-4, 4-6, 6-3 a zagaye na hudu.
Sau 22 Nadal dan asalin kasar Sifaniya ya lashe manyan gasar Tennis ta duniya a matakai daban-daban.
Tiafoe, mai shekaru 24, dan asalin jihar Maryland ne, ya kai zagaye na quarterfinal a karo na biyu a tarihin wasanninsa.
Wannan nasara ta Tiafoe da ta zamo abin mamaki ga masoya kwallon Tennis a duniya, na zuwa ne kwana guda, bayan da Nick Kyrgios ya doke Daniil Medevedev, wanda shi ne dan wasan Tennis na daya a duniya daga gasar wacce shi ke rike kofin.
Idanun Tiafoe sun rufe da hawaye farin ciki a lokacin da wasan ya zo karshe, wani abu da shi kansa ya kalla a matsayin almara – a ce ya doke Nadal
“Ji na yi kamar duniya ta tsaya cak, ban jin komai na tsawon minti daya.” In ji Tiafoe
Tiafoe shi ne na 26 a iya buga kwallon Tennis a duniya, yayin da Nadal shi ne na uku. Iyayen Tiafoe ‘yan asalin kasar Saliyo ne da suka yi kaura zuwa Amurka.