Na hannun daman Shugaba Buhari kuma ministan zirga zirgan jiragen sama yace ya ziyarci Shugaban a London.
Yace yana nan lami lafiya yana jiran sakamakon binciken da likitoci suka yi ne. Inji shi idan aka kawo maganar wannan ya ganshi wannan bai ganshi ba sai wata magana kuma ta taso, kamar ana boye wani abu ne.
Yace ya ga shugaban kasa kuma sun yi hira sun sha shayi tare, sun kuma karanta jarida tare, kuma duk abin da ake yi a Najeriya babu wanda shugaban bai sani ba. Yace suna magana da mataimakinsa mai rikon kwarya a kullum.
Hadi Sirika yace baya son ana dinga maganganu saboda haka aka fara yi a lokacin Shugaba Umaru Musa 'Yar'addu'a. Yace shugaba na nan lafiya. Zai gama binciken kuma zai koma gida Najeriya.
A bangaren majalisar dokoki da ta amshi takardar bayani daga shugaban Dan Majalisa Musa Sarkin Adar yace shugaban ya mutunta tsarin mulki.Yace kada a manta a lokacin shugaba Yar'addu'a da ya tafi neman magani bai rubutawa majalisa ba kuma bai mikawa mataimakinsa ragamar mulki ba. Abun da ya kawo cecekuce ke nan a kasar. Amma shugaba Buhari ya sanarda da majalisa ya kuma mikawa mataimakinsa mulki kuma komi na tafiya daidai. Yace yanzu ya rage ga jama'a suyi masa fatan alheri a duk inda yake.
Shugabannin al'umma da kungiyoyin addini na yiwa shugaban addu'ar samun karfin jiki domin ya koma bakin aikinsa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5