Gasar cin kofin duniya da ake cigaba da gudanarwa a kasar Rasha, yana daukar sabon salo, ganin yadda aka kaddamar da sabon tsarin mataimakin alkalin wasa “Rsferee” a wannan karon an maida hankali matuka wajen ganin yadda wannan sabuwar na’urar zata taimaka, wajen magance matsaloli da kan iya tasowa a lokacin wasa.
A wannan karon alkalan wasannin zasu maida hankali wajen amfani da sabuwar na’urar, don bibiyyar yadda wasa ya kasance, ko dai wajen warware wata matsala da ake ganin ta auku, ko kuma wajen kawo maslaha da fahimta.
“Muna maida hankali matuka ga wannan sabuwar na’urar” a cewar kocin Poland Adam Nawalka, kuma “Kimiyyar zamani tana taimakawa sosai don ganin yadda abu ya auku, hakan na kara muna yakini akan yadda muke gudanar da aikinmu.”
A karon farko kenan da kungiyar FIFA ta fara amfani da wannan na’urar da sabon tsarin da keba alkalan wasa da mataimakan su mutane na bayan fage damar ganawa kai tsaye yayin da wasa ke gudana. An tabbatar da na’urorin na aiki yadda ya kamata da ganin sun bada bayanai masu sahihanci.