WASHINGTON D.C —
A kasar Amurka, an kirkiro wata sabuwar na’ura mai kwakwalwa da aka yi wa lakabi da Super Computer, wadda aikin ta ya nunka na wadda ake amfani da ita a yanzu.
Ita dai wannan na’ura zata iya sarrafa bayanan lissafi Tiriliyan 200,000 cikin sakan guda.
Za a fara amfani da ita ne wajan fadada bincike a bangaren binciken magungunan cutar sankara ko kansa, da binciken ilimin tsirrai da makamantan su.
Wannan na’ura ko (Super Computer) a turance tana da girma da kuma da kuma tsadar gaske, domin tana dauke da manhajoji masu matukar muhimmanci da dama sa’annan kuma tana da sararin ajiye bayanai mai tarin yawa.