Yau tallata Trump, ya aika da wani sako ta kafar "twitter" ya na cewa ya so ne ya yada abin da ya kira, "gaskiyar abin da ake ciki game da ta'addanci da tabbatar da lafiyar tafiya ta jirgin sama" sannan ya yi kira ga Rasha da ta kara himma wajen yaki da ISIS.
Da alamar Trump, na mai da martani ne kan rahotonnin, wadanda aka yada da daren jiya Litini, ya na mai cewa a matsayinsa na Shugaban kasa ya na da cikakken hurumin bayyana irin wadannan bayanan.
Kafafen labaran Amurka da dama ne suka bayyana cewa Trump ya tattauna bayanan, wadanda ake ganin na sirri ne masu matukar muhimmanci, a yayin ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov, da Jakada Sergey Kislyak.
Rahoton na nuna alamar Trump, na alfaharin bayyana wasu bayanan sirri game da wani hadarin da ke tafe wanda ka iya shafar zirga-zirgar jiragen sama a cewar jaridar Washington Post.
Jaridar New York Times ta ce bayanan, wadanda aka ce na sirri ne sosai, ba a ma yada su sosai ga hukumomi a Amurka ko kuma ga kawayen Amurka ba.