Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Macron Ya Nada Edouard Philippe a Matsayin Firayim Minista


Sabon Firayim Ministan Faransa Edouard Philippe (
Sabon Firayim Ministan Faransa Edouard Philippe (

Sabon shugan kasar Faransa ya bayyana sunan Edouard Philippe, wani dan siyasa mai sassaucin ra’ayi, a matsayin sabon Firayim Ministansa.

Philippe dan shekaru 46, dan majalisar dokoki ne kuma Magajin Garin birninLe Havre ne. Yana daya daga cikin masu sassaucin ra’ayi na jam’yyar Republican ta Faransa.

An nada shi ne kwana daya bayan Macron ya karbi ragamarmulki a wani shagalin da aka yi na rantsar da shi a Paris.

Dan shekaru 39, Macron shine shugaban kasar Faransa mafi kankantar Shekaru.

A jawabinsa na ranar rantsarwa, yayi alkawarin dawo da martabar Faransa a idon Turai da kuma duniya baki daya. Ya kuma yi alkawarin cigaba da yaki akan ta’addanci.

An zabi Macron mai sassaucin ra’ayi, inda ya kada ‘yar takara Marine Le Pen mai adawa da Tarayyar Turai kuma, mara son baki daga kasashen waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG