Na Kafa Kamfani Sanadiyar Horaswar VOA

Aisha Umar Tofa , matashiya da ta kammala karatun ta na digiri kuma daya daga cikin daliban da muryar amurka ta horas a bara, na shirin sana’oin dogaro da kai

Matashiyar ta bayyana cewa sanadiyar horon da aka basu sun kafa kamfani, kuma suna biya wa kamfanin haraji wanda suka sawa suna a kimiyance.

Ta ce su bakwai ne suka yi hadin gwiwa wajen bude kamfanin, inda suke tallace-tallacen da ake sawa a gidajen talabijin da jaridu, har ta kai ga sun fara samun alfanu mai yawa.

A'isha ta ce tun bayan bude kamfanin wasu matasa biyu sun zo neman aiki a kamfanin nasu , amma kasancewar basu yi karfin da zasu dauki ma’aikata da zasu dinga biya ba, sun ja matasan a jiki sun kuma basu damar amfani da kamfanin domin inganta sana’oinsu

Daga cikin kalubalen da suke fuskanta, matashiyar ta ce rashin wadatattun kudi da zasu basu damar inganta sana’ar na daga cikin babban abin da ke ci masu tuwo a kwarya.

Your browser doesn’t support HTML5

Na Kafa Kamfani Sanadiyar Horaswar VOA