Wannan hukuncin ya fuskanci nuna bacin rai daga ciki da wajen kasar inda masu suka, suka bayyana shi a matsayin hari kan 'yancin 'yan jarida.
Jiya Litinin, wani alkalin kotun yankin arewacin Yangon ya samu Wa Lone da Kyaw Soe, da laifin karya dokar sirrin kasar, dokar da aka kafa tun ana kiran kasar da sunan Burma a lokacin mulkin mallakar birtaniya.
Dokar ta tanadi hukuncin daurin a kalla shekaru 14 a gidan kaso.
An kama 'yan jaridun ne a watan disamba a yankin Yangon da ke arewacin kasar lokacin suna binciken zargin kisan da aka yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a wani kauye da ke jihar Rakhine a arewacin kasar.
Wa lone da Kyaw Soe Oo, sun ce wani ne ya ba su wasu takardu wanda daga bisani 'yan sanda suka gayyace su liyafar cin abinci suka kama su.
Lauyoyin gwamnati sun hakikance akan cewa an kama wadanda ake zargin ne a lokacin wani sintiri da jami’an tsaro suka saba yi, inda aka samo takardun.