Wannna muhawara ta gudana ne yayin da ya rage kasa da kwanaki uku a yi zaben New Hampshire a yunkurin fitar da dan takarar da zai wakilci jam’iyar a zaben karshen shekarar nan.
Daga cikinsu dai babu wanda ya fi fusata kamar gwamnan New Jersey, Chris Christie, wanda ya yi ta caccakar Sanata Marco Rubio a farkon muhawarar, inda ya ce ba shi da kwarewar da zai iya zama shugaban kasa.
A daya bangaren kuma hamshakin attajiran nan Donald Trump, ya fi maida hankali ne akan matakan da ya ke so ya dauka game da batun bakin haure, ciki har da batun gina Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, kana ya ce zai maida hankali sosai wajen yaki da kungiyar ISIS.
Shi kuwa Ted Cruz wanda ya zo na farko a zaben Iwoa, cewa ya yi akwai bukatar hare-haren da ake kaiwa a Syria da Iraqi, su kasance sun maida hankali kan ‘yan ta’adda ba kowa-da-kowa ba.