.Muhawarar ta zo ne kwanaki kadan kamin jihar dake arewa maso gabashin Amurka ta gudanar da zaben share fage na fidda dan takara shugabancin kasa.
A jihar New Hampshire Madam Clinton tana baya da Sanata Bernie da maki 20,bayan da kiris ta doke shi a 'yar tinken da aka yi a jihar Iowa. Wannan muhawarar itace ta farko da 'yan takarar suka yi su biyu kadai, bayanda tsohon gwamnan jihar Maryland Martin O'Mally ya janye daga takarar, saboda bai tabuka komi ba a 'yar tinken da aka yi a Iowa.
Yanzu ganin masu zabe sun fara bayyana wanda suke so, yakin neman zaben da a baya ake dasawa,yanzu an fara zafafa kalamai, inda Madam Clinton d a Sanata Sanders suna ta cacar baki kan ko wanene mai ra'ayin ci gaba tsakaninsu, wanene masu hanu da shuni suke da iko da shi, kuma kan ko menene barazanar da Amurka take fuskanta.
Clinton, mai shekaru 68 da haifuwa, tana kiran kanta 'mai ra'ayin ci gaba, mai fada da cikawa,' tana mai cewa kudurorin Sanata Sanders, na bada ilimi kyauta, da kiwon lafiya, alkawura ne da ba za'a iya cikawa ba.