Cibiyar nazarin matsalolin abinci ta duniya ta yi hasashen mutane kimanin miliyan bakwai ne za su fuskanci matsalar yunwa a Najeriya a cikin watannin Yuni da Yuli da kuma Agustan wannan shekara.
WASHINGTON DC —
Rahotan na nuni da cewar daga cikin rukunin mutanen da zasu fuskanci karancin abinci, har da yara kananan wanda zasu fuskanci rashin samun abinci mai inganci da zai gina musu jiki.
Ita dai wannan cibiya na fitar da rahotanta a kowacce shekara domin gargadin hukumomi da kuma gwamnatoci su tabbatar sun dauki matakan kwarai don tinkarar matsalar.
Matsalar tsaro a sassan Najeriya da gurbatar muhalli da kuma bayyanar cutar coronavirus na daga cikin dalilan da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce zasu janyo karancin abinci.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5