Kungiyoyin fafutukar kare mata da yara da dama na ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara kaimi wajen yaki da matsalolin ‘yan bindiga dadi da ke yi wa mata fyade baya ga kashe mazajensu a jihar Katsina.
Kungiyar Lawal Dan Alhaji da mambobinta, sun gudanar da wata zanga-zanga a dandalin Unity da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, inda wata 'yar kungiyar da ta bukaci a sakaya sunanta ta yi kira ga gwamnati akan ta kai wa al’umma dauki duba da yadda ake yi wa iyaye mata fyade a gaban ‘yayansu.
A na ta bangaren shugabar kungiyar Lawal Dan Alhaji, Halima Mukhtar, ta bayyana cewa ba zasu dora wa gwamnati laifi ba sai dai su yi kira a kan gwamnatin ta saurari koken al’ummar Batsari.
Wani da ya shaida abubuwan ke faruwa a Katsina ya ce mutanen Batsari na cikin tashin hankali sakamakon yadda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke cin karen su babu babbaka.
Hakazalika, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Commission, Tony Ojukwu, ya ce kungiyarsu ta fara gangamin wayar da kan al’umma a kan matsalolin da suka shafi fyade da na jinsi tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki su zo a hada karfi da karfe da gwamnatin a dukkan matakai saboda a kawo karshen matsalolin da suka addabi al’umma.
Matsalolin ‘yan bindiga a arewacin Najeriya na kara tsananta, lamarin da ya tilasta wa manoma da dama kaurace wa gonakinsu saboda gudun tsira da rai.
Sai dai masana a fannin aikin noma sun yi gargadi a kan tasirin rashin noma ga al’ummar kasar ganin yadda annobar coronavirus ta gurgunta ayyukan kasuwanci.
A ranar Laraba 17 ga watan Yuni, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tura tawagar hukumomin tsaron kasar zuwa jihohin Katsina da Sokoto, domin lalubo sabbin dabarun aiki na kawo karshen matsalolin tsaro da fyade a kasar.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf:
Facebook Forum