Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki shugabbanin tsaro bisa yadda suke aiwatar da ayyukansu, ganin yadda ake ta kai hare-hare a arewacin Najeriya.
A cewar shugaban, dole sai an kara kokarin da ake yi wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar.
Babban mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ne ya bayyana kalaman shugaban jim kadan bayan da Buhari ya gana da shugabbanin na tsaro a yau Alhamis.
Wadannan kalaman na shugaban sun kasance kalamai mafiya kaushi game da salon shugabbanin na tsaro a arewacin Najeriya, a daidai lokacin da yanayin tsaro ke kara muni.
A cewar Mongonu shugaban Najeriya ya nuna matukar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara muni a kasar.
“Shugaban kasar yana ganin duk da cewar hukumomin tsaro na kokari, kokarin nasu bai isa ba wajen cimma burinsu cikin gaggawa,” a cewar Mongonu.
Tun a shekarar 2015 ne aka samu kau da Boko Haram daga yawancin yankunan da ta mamaye amma duk da hakan kungiyar ta ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya da kasashen Nijar da Kamaru.
A ranar Lahadi ma wasu mayaka sun kashe akalla mutum 60 a Borno, kwanaki kadan aka sake kai wani hari a yankin, inda mutum 69 suka rasa rayukansu.
A cikin watan Mayu, Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashin hankali ya sa mutum 23,000 sun gudu daga Najeriya zuwa Nijar cikin mako daya.
Facebook Forum