Hotunan da kafafen yada labarai na Indiya suka wallafa sun nuna tarkacen jiragen kasan a jere a gefe, inda daya daga cikin su, ya fada a kan dayan bayan karon.
'Yan sanda sun ce masu aikin ceto na ci gaba da duba tarkacen ko za a samu karin mutane da suka makale a kasa.
Iftikar-Ul-Hassan ‘dan sanda a yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Mun samu tabbacin mutuwar mutane bakwai da fasinjoji 39 da aka kwantar a wani asibitin yankin da raunuka daban-daban."
Lamarin dai shi ne na baya-bayan nan da ya afku a layin dogo na Indiya, wanda ke daukar miliyoyin fasinjoji a kowace rana.
Rajesh Kumar Singh, daga Rundunar Kariya ta Layin Jirgin Kasa, ya shaida wa AFP cewa: "Mun ga gawar wani direban da ya mutu da kuma mai gadi.” "Wasu karin gawarwakin na iya kasancewa a karkashin wurin da hadarin ya auku, amma har yanzu ba mu tabbatar ba.
Firaiminista Narendra Modi ya yi ta'aziyya ga "wadanda suka rasa 'yan uwansu", a cikin wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya kara da cewa "ana ci gaba da ayyukan ceto".
Babban Ministan Yammacin Bengal Mamata Banerjee ya kira hadarin "abin takaici" a wani sako da shi ma ya wallafa a shafukan sada zumunta.
"An garzaya da likitoci, motocin daukar marasa lafiya da kungiyoyin bada agaji zuwa wurin don aikin ceto, da kuma jinya, in ji Banerjee.
-AFP