Mutum 24 Sun Mutu A Jihar Kano Sakamakon Cutar Mashako

Wata yarinya a Asibiti ta na kuka.

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da bullar cutar Mashako (Diphtheria) a jihohi hudu na fadin kasar.

Jihohin da aka tabbatar da bullar cutar sun hada da jihar kano, legas, Yobe da kuma Osun.

A bayanan da take fitarwa game da cututtukan da aka samu bullar su a kasar hukumar NCDC, ta ce a kalla mutum 34 ne suka mutu a fadin kasar sanadiyyar cutar ta Mashako.

Shugaban hukamar NCDC Ifedayo Adetifa ya ce rashin karbar rigakafi na daga cikin abubuwan da yasa aka samu cutar a Najeriya.

Kwararren likita Dr. Lawal Musa Tahir ya ce cutar na farawa ne da mura da kuma zazzabi da bashi da tsanani.

Dr. Lawal ya kara da cewa cutar tafi kama yara yan kasa da shekaru biyar da kuma manya da suka haura shekara arba'in, ya kuma ce cutar ta na kisa.

A nasa Bangaren, daraktan tsare-tsare da binciken kididdiga na hukumar lafiya matakin farko a Abuja Dr. Abdullahi Bulama Garba, ya tabbatar da cewa akwai rigakafin cutar, kuma hukumar na aikin wayar da kan jama'a game da muhimmancin yin rikagafi.

Hakan dai ya biyo bayan yaki da kasar Najeriya ke yi ne da cututtuka kamar Cholera, Zazzabin Lassa, Zazzabin cizon sauro da kuma cutar coronavirus.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutum 24 Sun Mutu A Jihar Kano Sakamakon Cutar Mashako - 2'33"