Mutanen Sudan ta Kudu Sun Yi Gangamin Kin Yakin Kasarsu Gaban White House

Gangamin kin yakin da ake yi a Sudan ta Kudu

'Yan asalin Sudan ta Kudu daban daban ne suka yi gangami gaban Fadar White House a nan Washington DC suna kiran a kawo karshen yakin kasarsu ko ta halin kaka

Masu zanga zanga yan kasar Sudan ta Kudu da masu fafutuka ta fuskar siyasa, da wadan suke da alaka da kungiyar adawar kasar ta SPLM ne suka yi cincirindu a gaban fadar White House a jiya Litinin domin nuna adawarsu ga yaki da ake yi a kasarsu.


Masu zanga zanga kimanin 25 ne suke ihu suna cewar "mutanen Sudan ta Kudu suna mutuwa kuma muna bukatar zaman lafiya a Sudan ta Kudu."


Da take jawabi da harshen Larabci, Elizabeth James da ta fito daga jihar Tennessee a nan Amurka, tace ana bata lokaci, yakamata a yi wani abu a kan matsalar Sudan ta Kudu.


Tace kada a kyale batun neman zaman lafiya a hannun gwamnati da yan tawaye. Tace zasu dauki lokaci na ganin damarsu saboda cimma bukatunsu.


A cikin watan Faburairu, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta aza takunkumin hana sayarwa Sudan ta Kudu makamai. Wannan haramcin bai yi wani tasiri sosai ba, ganin Amurka bata sayarwa Sudan ta Kudu makamai dama can. Amma dai takunkumin ya hana duk wani kampanin Amurka ko wani Ba-Amurke sayarwa kowane bangare masu yaki da juna makamai.