Wata tanka shake da mai ta fadi a garin Akamkpa, cikin karamar hukumar akamkpa ta jihar Cross River inda mazauna yankin suka rika yin tururuwa domin jidar man dake malala a kasa ba tare da kakkautawa ba.
Wani bidiyon al’amarin daya karade shafukan sada zumunta da safiyar yau Alhamis ya nuna yadda mazauna garin ke jidar man dake kwarara daga tankar dake kwance a gefen hanya.
An ga wasu daga cikin mutanen dauke da bukitai, a yayin da wasu ke amfani da mazubai daban-daban wajen jidar man daga tankar.
Duk da cewar babu wani rahoto a hukumance daga direba ko al’ummar gari game da abin da ya sabbaba hatsarin, amma ba’a samu asarar rai ba.
Kuma har yanzu hukumomin jihar basu ce komai game da al’amarin ba.
Faruwar lamarin na kara sabbaba damuwa, musamman bayan mutuwar kimanin mutane 180-dake jidar man fetur daga wata tanka da ta fadi a jihar Jigawa.
Ku Duba Wannan Ma Fashewar Tankar Mai: Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Jigawa Ya Karu Zuwa 170