Mutane Uku Sun Mutu A Hadarin Helikwafta A Fatakwal 

Sanarwar da mahukuntan kasar ta fitar ta ce, jirgin ya kutsa cikin ruwan da ke kusa da Bonny Finima a cikin Tekun Atlantika, kuma ta kara da cewa tuni an fara aikin ceto. 

Ma'aikatar sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya ta tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane uku a wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Hatsarin ya afku ne a ranar Alhamis 24 ga Oktoba, 2024 a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Hatsarin ya afku ne da misalin karfe 11:22 na safe a kan magudanar ruwa a Fatakwal, lokacin da jirgin mai saukar ungulu kirar Sikorsky SK76 mai lamba 5NBQG yana kan hanyarsa daga makarantar sansanin soji ta (DNPM) zuwa tashar mai na Nuimantan.

An tabbatar da cewa mutane takwas ne ke cikin jirgin, in ji mai magana da yawun ma’aikatar sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Odutayo Oluseyi.

Sanarwar da mahukuntan kasar ta fitar ta ce, jirgin ya kutsa cikin ruwan da ke kusa da Bonny Finima a cikin Tekun Atlantika, kuma sanarwa ta kara da cewa tuni an fara aikin ceto.

Ma’aikatar ta ce an sanar da Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) da dukkan hukumomin da abin ya shafa, inda ta ce an fara aikin bincike da ceto tare da tallafin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), da sauran hukumomin da abin ya shafa.

~Yusuf Aminu Yusuf