Har yanzu dai hukumar jiragen kasa ta Najeriya ba ta fitar da takamaiman alkaluman wadanda aka kashe da kuma wadanda 'yan-bindigan suka sace ba.
Sai dai ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasan daga Abuja zuwa Kaduna har sai an tantance barnar da harin ya yi.
Ita kuwa gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kammala aikin kwashe mutanen da harin 'yan-bindigan ya rutsa da su.
Wasu daga cikin matan da 'yan-bindigan suka harba kuma suke kwance a asibiti, sun yi mana karin bayani kan yadda abun ya faru, inda suka ce suna zaune sai su ji wani kara mai karfi daga jirgin, daga nan sai jirgin ya kauce layi, sannan suka fari jin harbe-harbe.
Sai ga 'yan bindigan sun fasa kofar masu hannu da shuni (VIP) suka shiga suka kashe wasu, sannan suka yi garkuwa da wasu.
Yanzu haka dai an fitar da jadawalin mutanen da su ka sayi tikitin tafiya a jirgin aka kaiwa harin abun da ya sa 'yan'uwan mutanen suka bazama neman su, kamar dai yadda wasu suka yi magana bayani a filin jirgin kasa dake Kaduna.
Daya da ga cikinsu ya ce dan uwansa har yanzu ba a ganshi ba, sai dai wayar kadai aka tarar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan-bindigan ke tare jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna ba sai dai kuma wannan ne karon farko da 'yan-bindigan suka kashe mutane sannan suka sace wasu duk kuwa da cewa wani shugaban al'uma da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar mana cewa sun sanar da hukumomi game da ganin 'yan-bindigan akan babura sama da dari uku (300) akan Danjibgan jihar Zamfara suka ketara zuwa Rijanan jihar Kaduna inda anan ne aka kai wannan harin jirgi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5