Mutane Na Kauracewa Yankin Kerawan Sabili Da Rashin Tsaro

'yan bindiga

Hare-haren 'yan-bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Kerawan karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna ya sa mutanen wasu kauyuka kauracewa garuruwan su zuwa garin Birnin Yero domin neman mafaka.

Daruruwan al'uma daga garuruwa daban-daban na yankin Kerawan da su ka taso sun yada zango ne a makarantar firamare dake Birnin Yero sun shedawa Muryar Amurka cewa, sun baro gidajen su ne karfi da yaji a irin wannan lokaci. Bisa ga bayanin su, an kona gidajensu da rumbunan abincin su. Su ka ce ‘yan bindiga suna yawan kai hare hare a yankin kuma sau da dama suna zuwa ne da rana tsaka su bude wuta kan al’umma su, wadandansu kuma su banke su da gangan.

mayakan-boko-haram-sun-fice-daga-garin-dikwa-na-jihar-borno

an-saki-yan-makarantar-kagara-da-malamansu

yan-bindiga-sun-kashe-mutum-6-tare-da-sace-wasu-15-a-jihar-neja

Mutanen da Muryar Amurka ta yi hira da su sun bayyana cewa, ba bu jami’an tsaro da su ke zagawa a yankin yanzu duk da yake ko a lokacin da su kan zagaya jefi jefi, ba su dakile kai hare haren ba.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce jami'an tsaro na iyaka kokarin su don kawo karshen matsalar tsaro a yankunan da abun ya fi shafa inji kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mal Samuel Aruwan.

Bisa ga cewar kwamishina Aruwan, aikin da jami’an tsaro ke yi ya shige hare haren da aka ji ana kaiwa.

Fulani masu garkuwa da mutane

Wannan dai shine karo na biyu da al'umar yankin Kerawa ke baro gidajen su saboda yawan hare-haren 'yan-bindiga a yankin.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Na Kauracewa Yankin Kerawan Sabili Da Rashin Tsaro:4:00"


Karin bayani akan: Kerawa, jihar Kaduna​, Birnin Yero, Nigeria, da Najeriya.