Mutane Na Bayyana Ra'yoyinsu Kan Shekara Daya da Buhari Ya Kama Mulki

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yayinda gwamnatin Buhari ke gaf da cika shekara daya da karban mulkin Najeriya mutane na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan mulkin na Buhari

Mutane da dama sun amince gwamnatin ta cimma nasara wajen karya lagwan 'yan Boko Haram wadanda suka addabi arewacin Najeriya musamman arewa maso gabashin kasar

Lamido Umar Cakere dan babban jam'iyyar adawa ta PDP yace inda waccan gwamnati ta kasa ko sabili da rashin kwarewa ko ganganci shi Muhammad Buhari inda ya kware ke nan kuma gashi ya yi nasara akan yaki da Boko Haram. Dalili kenan idan za'a ba mutum aiki a bashi inda yake da kwarewa da ilimin abun ba a yi da son zuciya ba.

Shi ma tsohon ministan lafiya da harkokin waje Idi Hong na ganin kasar ta doru akan turbar nasara. Yace kamar shi da ya fito daga yankin da ya sha fama da rikicin Boko Haram gashi yanzu an soma samun zaman lafiya wanda babban cigaba ne.

Yace abu na biyu alkawarin yaki da cin hanci da rashawa nan ma ana samun galaba. Sabili da haka an kwato kudade masu yawa daga wadanda suka sacesu. Idan kuma aka bada lokaci akwai shirye-shirye da zasu kaiga biyan bukatun 'yan kasa. Yace can baya an ruguza kasar.Dole ne yanzu a dauki lokaci wurin sake ginata.

Amma a nashi ra'ayin dan canjin kudi Jubril Zaka yana tababan nasarar da gwamnatin ta cimma. Yace jam'iyyar adawa tayi mulkin shekara 16 ana ta cewa an sace kudi amma yanzu wane kare ne ba bula ba? Yace kusan kashi 65 na gwamnatin yanzu daga PDP suka koma APC domin biyan bukatunsu.

Alhaji Musa Yola wani dattijo yace wasu 'yan Najeriya sun faye gaggawa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Na Bayyana Ra'yoyinsu Kan Shekara Daya Ta Mulkin Buhari - 3' 03"