DSP Zubairu Abubakar wanda ya kasance kakakin rundunar 'yansandan shi ya yiwa manema labaru bayani.
Yace mutanen barayi ne masu fashi da makami da sace motoci da kuma sace mutane ko yin garkuwa dasu domin samun fansa. Cikinsu ma akwai masu sace shanu.
Masu fashi da makami da kuma kwace motoci da makamai sun kai su ishirin. Barayin sun hada da mata biyu da suke ajiye masu bindigoginsu
Wajen su goma sha biyu ne suke garkuwa da mutane. Akwai kuma masu satar shanu su takwas.
'Yansandan sun samu bindigogi da harsashai a wurin wadannan muggan mutanen. Yanzu dai 'yansanda na cigaba da bincike bisa ga abubuwan da muggan mutanen suka gaya masu domin su kamo wadanda yanzu basu shiga hannu ba tukunna.
To saidai wasu cikin barayin an sha kamasu ana kaisu kotu kuma sai su dawo su cigaba da barnar da suka saba yi. Dalili ke nan da kwamishanan 'yansandan jihar yace zai yi magana do kotuna da su taimaka.
Wasu daga cikin wadanda aka cafke da zargin tafka manyan laifuka sun amsa da kansu. Wani cikinsu ya bayyana yadda 'yanuwansa suka sassare mutumin da suka yi garkuwa dashi.Shi kuwa Inusa dan shekara ishirin daga karamar hukumar Kubau yace bana suka fara satar mutane. Ya kuma fada cewa suna yin anfani da bindigogi suna sata akan hanyoyi kamar akan hanyar Abuja zuwa Lafiya ko Jere da misalin wajejen karfe bakwai na yamma.
Su dai wadan nan muggan mutanen sun shaida cewa babbansu ne ya sayo masu bindigogi daga Libya.
Ga karin bayani.