Mutane kalilan su ka fito zaben shugaban kasar Kamaru

  • Ibrahim Garba

Shugaba Paul Biya na Kamaru

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi kira ga mutanen kasarsa das u

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi kira ga mutanen kasarsa das u kula sosai da duk wani kuskure a tasrin zabe, a yayin day a ke kada kuri’arsa a zaben Shugaban kasar a jiya Lahadi.

Kodayake mai yiwuwa ba za a sanar da sakamako ba har sai bayan sati biyu, ana kyautata zaton Mr. Biya zai ci sabon wa’adi na tsawon shekaru 7, wanda zai tsawaita mulkinsa wanda ya kai shekaru 29 ya na yi zuwa yanzu a wannan kasa ta yankin tsakiyar Afirka.

Mr. Biya y ace babu wani daidai a duniyar nan, y ace to amman ko da an sami wata mishikila, ba da gangan aka yi don makudi ba. Yan a karawa ne da sauran ‘yan takara 22, wanda ba a taba ganin ‘yan takara masu wannan yawar ba. Wanda ya fi fice wurin ja das hi, John Fru Ndi na Jam’iyyar Social Democratic Front, ya sami kashi 17% na kuri’un a 2004.

Masu sa ido kan zaben sun ce an sami karancin masu kada kuri’a sosai a jiya Lahadi, bayan ‘yan Kamaru da dama sun yi ta nuna halin ko in kula, sun a cewa an riga an yanke shawara kan wanda zai ci.

Ba a sami adadin fitowa a kasar baki daya ba, to amman masu sa ido kan zaben sun ce a wasu wuraren zaben ma wadanda su ka yi rajista kasa da 15% su ka fito zaben.

An kuma fara zaben a makare a wasu wurare. A wasu wuraren har ma lattin sa’o’i aka yi. Kuma wasu masu kada kuri’a sun shaida wa kamfanin dillancin Labaran Associated Press cewa an bas u fiye da katunan zabe daidai, wanda hakan zai bas u damar yin zabe fiye das au daya.

Jiya Lahadi wasu ‘yan bindiga dab a a san ko su waye ba sun kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu a yankin Bakassi mai arzikin man fetur.