Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaben Shugaban Kasa a Kamaru


Wata mai goyon bayan shugaban kasar Kamaru Paul Biya, a birnin Yaounde ranar jajiberen zaben shugaban kasar
Wata mai goyon bayan shugaban kasar Kamaru Paul Biya, a birnin Yaounde ranar jajiberen zaben shugaban kasar

Ana ci gaba da zaben shugaban kasa a Kamaru wanda ake kyautata cewa Paul Biya ne zai lashe wani wa'adin shekaru bakwai.

Zaben shugaban kasar Kamaru na gudana sannu a hankali a yau lahadi , kuma ba a bude rumfunan zabe da wuri ba kamar yadda aka zata.

Ana kyautata cewa shugaban kasar Kamaru mai ci yanzu, Paul Biya shi ne zai lashe wani wa’adin mulkin shekaru bakwai, wanda hakan zai tsawaita mi shi mulkin shi na shekaru 29 a kasar ta Kamaru.

Shugaban mai shekaru 78 ya na fuskantar wata hamayyar da ba ta karfi, mai ‘yan takara 22 a zaben.

John Fru Ndi na jam’iyyar Social Democratic Front ko Front Social-Démocratique shi ne babban abokin hamayyar shugaba Biya, wanda a zaben shekarar dubu biyu da hudu ya samu kashi 17 cikin dari na kuri’un da aka kada a kasar.

Da kashi 70 cikin dari Mr.Biya ya lashe zaben na shekarar ta dubu biyu da hudu.

‘Yan hamayyar kasar sun zargi hukumar zaben kasar Kamaru da fifita jam’iyyar da ke mulkin kasar kuma an yi ta yin korafe-korafen kurakurai a rajistar masu zabe.

Wasu ‘yan kwanaki kalilan kafin zaben na yau lahadi an kori wani babban jami’in hukumar zaben kasar Kamaru Elecam, bisa zargin shi da yiwa shugaba Biya yakin neman zabe wanda yin hakan ya karya ka’idar aikin hukumar.

Mr.Biya ne ke mulkin kasar Kamaru tun shekarar 1982. A shekarar dubu biyu da takwas ya soke dokar takaita wa’adin mulkin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, don ya samu damar sake tsayawa takara a zaben bana. Wannan taku na shugaban kasar ya takalo zanga-zanga a kan titunan kasar wadanda su ka yi sanadiyar mutuwar mutum 40 a kalla.

‘Yan kasar Kamaru masu yawan gaske na cikin halin kunci rashin aikin yi da kuma karuwar tsadar rayuwa.

XS
SM
MD
LG