A kalla mutane 23 ne aka kashe wasu kuma 150 su ka sami raunuka a jiya Lahadi a al-Khahira babban birnin Misra, bayan da wata zanga-zangar da Kirista ‘yan darikar Kuftawa su ka yi, don nuna bacin ransu game da kona wata Majami’arsu da aka yi kwanan nan, ta yi tsanani ta zama ta yin bore ga mulkin soji.
Masu zanga-zanga sun yi ta jifa da kayan fashe-fashe, da kona motocin soji, su ka yi ta fafatawa da jami’an tsaro a tashin hankalin da ya fi muni tun bayan boren cikin watan Fabrairun da ya kai ga hambarar da tsohon Shugaba Hosni Mubarak.
Daruruwan masu zanga-zanga sun fafata da ‘yan sanda, wasunsu sun yi ta balle daben siminti da daukar duwatsu suna ta jifa das u. Ana cikin dauki ba dadin sai wata motar jami’an tsaro ta sheko a guje, ta markade wasu masu zanga-zangar har lahira. Wasu sojoji 2 ma sun mutu a tashe-tashen hankulan na jiya Lahadi.
Kirista masu zanga-zanga sun ce wani gangami ne das u ka yi cikin lumana a unguwar Kuftawa ta Shubra ya kazance, bayan da wasunsu su ka yi maci zuwa gidajen Rediyo da Talabijin din Misra, a inda ‘yan sandan farin kaya su ka far masu. Daga bisani zanga-zangar ta wanzu zuwa Dandalin Tahrir, inda nan ne cibiyar juyin juya halin watan Fabrairu.
Kafofin yada labaran gwamnati sun ce gwamnatin wuccin gadin Misra na wani taron gaggawa don tattauna lamarin. Sojoji sun kafa dokar hana zirga-zirga da dare a harabar Dandalin Tahrir da kewaye.
Cikin ‘yan makonnin da su ka gabata, tashe-tashen hankula sun barke a harabobin wasu majami’u biyu a kudancin Misra, bayan da wasu Musulmi su ka yi zanga-zanga saboda gina Majami’a.