Mutane goma aka kashe a wani harin da kungiyar Taliban ta kai Afghanistan

Wani dan sandan kasar Afghanistan ne yake gadi a mararrabar data doshi otel din da aka kaiwa hari a birnin Kabul.

Jami'an kasar Afghanistan sunce an kashe mutane goma a sakamakon harin da kungiyar Taliban ta kai wani kasaitattacen ote a Kabul baban birnin kasar. Wannan adadi bai hada da akalla masu harin kunar bakin wake guda shidda da suma suka mutu ba.

Jami’an kasar Afghanistan sun ce farar hula goma aka kashe, a sakamakon harin da kungiyar Taliban ta kai wani kasatattacen otel jiya talata da dare a Kabul baban birnin kasar.

Jami’ai sun fadi da safiyar yau Laraba cewa adadin wadanda suka mutu, bai hada da akalla masu harin kunar bakin wake guda shidda ba, wadanda au sun tarwatsa kansu ko kuma jami’an tsaro ne suka kashe su.

Da sanyin safiyar yau Laraba mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Wajen kasar, Siddiq Siddiq ya bada sanarwar cewa an kawo karshen kawanyar da aka yiwa otel din na tsawon sa’o’i hudu, yana mai fadin cewa motocin jami’an tsaro da kuma motocin daukar mara lafiya suna ta kwashe gawarwaki da wadanda su ka ji rauni daga otal din.

Kungiyar Taliban tayi ikiran cewa ita keda alhakin kai harin, ta kuma ceta tana auna ‘yan kasashen waje ne, Ma'aikatar harkokin wajen Amirka tayi Allah wadai da harin, tana mai fadin cewa wannan mataki ya kara nuna yadda kungiyar Taliban bata dauki rai a bakin komai ba.