Sabuwar shugabar asusun IMF tayi alkawari gudanar da harkokin asusun kamar yadda aka yi a lokacin rikicin kudin duniya. Ministar kudu ta Faransa, Christine Lagarde, wadda talatan nan aka nada ta a zamar shugabar asusun IMF ta fada a wata sanarwa cewa, tilas asusun IMF ya zama mai tasiri da muhimmanci da sauraron bukatun kasashe da kuma gudanar da aiyukansa yadda ya kamata, domin a cimma burin bunkasa wa kasashen asusun dari da tamadin da bakwai, tattalin arzikinsu
Karkashin wata yarjejeniya da aka kula ba a hukunce ba, duk wanda ko wadda zata shugabanci asusun IMF tilas ta fito daga wata kasar turai yayinda shugaban bankin duniya kuma ya zama Ba Amerike. To amma shugabanin kasashe, irinsu Brazil da India da China da kuma wasu kasashe wadanda ke kara taka muhimmiyar rawa a bunkasar tattalin arzikin duniya, sunce wancan tsarin ya zama tsohon yayi.
Ita dai Christine Lagarde, wadda ta zama macen farko data dare kan wannan mukami, tun shekara ta dubu biyu da bakwai take mukamin Minister kudin Faransa. A ranar biyar ga watan Yuli idan Allah ya kaimu, zata fara wannan aiki na wa'adin shekaru biyar