Mutane Dari da Goma Sha Takwas ne Suka Mutu a Jos

Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe a birnin Jos, dake Jihar Filato.

yanzu haka kura ta lafa ana kuma samun kwanciyar hankali a garin Jos.
Jami'an tsaro a Najeriya, sun yi bayanin cewar an gano gawarwakin mutane dari da goma sha takwas ta wadanda harin bomo-bomai ya rytsa dasu a Jos.

Boma-bomain sun tashi ne a lokacin cunkoson jama'ar dake cinikayya a kasuwar Taminas a Jos,babban birnin jihar Filato.

Amma a yanzu haka kura ta lafa ana kuma samun kwanciyar hankali kasancewar yanda jami'an tsaro ke ta gudanar da sintiri a lungu da sako na garin Jos.

Kan bom din da ake zargi an samu a anguwar Tudun wadan Jos kwamishinar 'yan sandan jihar Chris Olape yace babu wani tabbaci aka.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane 118 ne suka Mutu a Jos -2'50"