Tun da misalin karfe bakwai na safe ne wasu masu jefa kuri’u suka ja layi a cibiyoyin zabe daban daban dake birnin Legas, ko da yake ba a fara zaben da wuri ba a wasu sassa, bincike ya nuna cewar jama’a a yau ma basu fito da yawa ba domin kada kuri’un nasu, idan akayi la’akari da katin zabe Miliyan biyar da jihar Legas ke tunkaho da shi.
Alhaji Ali Aware Mahmud Inuwa Garin Malam, wani Dattijo ne dake zaune a unguwar iddi’harba ya ce yana kira ga jama’a dasu fito suyi zabe lafiya, su a tashi lafiya, kuma wanda yayi nasara a bashi. Kuma yana kira da hukumar zabe ta INEC su dinga kawo zaben akan lokaci.
A bangaren kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas Alhaji Ma’azu Zubairu, ya shaidawa wakilin muryar Amurka Babangida Jibril ta wayar tarho cewa, ana gudanar da zaben kamar yadda ya kamata ba tare da wani rikici ba a jihar ta Legas, sabanin abin da ya faru a lokacin zaben shugaban kasa da ya gudana, inda aka sami tashin hankali musamman tsakanin kabilar Yarabawa da kabilar Igbo.
Saurari cikakken Rahoton Babangida Jibrin daga Legas.
Your browser doesn’t support HTML5