Mutane Biyu Sun Mutu Wasu Da Dama Sun Jikkata A Wani Harin Masallaci A Portugal 

Mutane Biyu Sun Mutu Wasu Da Dama Sun Jikkata A Wani Hari A Masallaci A Portugal

‘Yan sandan Portugal sun harbe wani mutum da ake kyautata zato ya daba wa wasu mata biyu wuka har lahira a wata cibiyar Musulunci ta Ismaili Muslim Center da ke Lisbon, a cewar hukumomi a ranar Talata. 

WASHINGTON, D.C. - Matan ma'aikatan ne a cibiyar ta Portugal, abin da shugaban Al'ummar Ismaili, Narzim Ahmad ya shaidawa gidan talabijin din Portuguese na S.I.C kenan.

An tura ‘yan sanda zuwa cibiyar da safiyar ranar Talata inda suka ci karo da wani mutum wanda ake zargi da aikata laifin dauke da “babbar wuka,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

Mutane Biyu Sun Mutu Wasu Da Dama Sun Jikkata A Wani Hari A Masallaci A Portugal

'Yan sanda sun bukaci ya mika wuya amma yayi kokarin afka musu, su kuma suka harbe shi, in ji sanarwar. An kai mutumin da ake zargi da aikata laifin zuwa asibitin Lisbon inda yake a karkashin kulawar ‘yan sanda.

Wasu mutane da dama sun jikkata, a cewar sanarwar, amma ba ta bayar da wani karin bayani ba.

Firai Minista António Costa ya ce 'yan sanda sun harbi wanda ake zargi da aikata kisan ya kuma fada wa manema labarai cewa harin babban "laifi ne."

-AP