'Yan bangan garin Kolofata sun nemi su kama 'yan matan yayinda suke kokarin kutsa kansu cikin wani masallaci da nufin tarwatsa kansu.
Jami'an tsaro sun harbe guda har lahira yayinda 'yan banga suka harbi dayar da kibiya inda ta tarwatsa kanta.
Harin ya zo ne daidai lokacin da gwamnoni goma da ministan harkokin cikin gida suka kammala taron inganta tsaro a duk fadin kasar ta Kamaru.
Shugaban kasar Paul Biya ya aika da sakon murnarsa ga jami'an tsaro da ma 'yan banga saboda irin jajircewar da su keyi na karawa da 'yan Boko Haram.
Ministan harkokin cikin gidan ya kira jami'an tsaro da 'yansanda su kara jan damara domin tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara cikin lumana da lafiya a duk fadin kasar. Ya kira masu bulaguro cikin safa safa da wasu motoci su ba jam'an tsaro hadin kai saboda binciken kwakwaf da ake yi masu..Ya kara da kira su tona asirin duk wanda basu yadda dashi ba. Ya ce zasu sanya jam'an tsaro a duk cikin motocin sufiri domin kare jama'a. Ministan ya gargadi gwamnonin da su yi aiki da sarakunan gargajiya da kungiyoyin sa kai.
Kungiyar direbobin sufuri ta kira gwamnati ta kara tsaro a jihohin arewacin kasar inda 'yan Boko Haram ke kai hari kodayaushe. Haka ma tana son a inganta tsaro a jihohin gabashin kasar saboda masu fashi da makami.
Ga karin bayani.