Yawan mutanen da suka mutu a mummunan a harin da aka kai da wata motar daukar kaya a Somaliya cikin watan Oktoba ya karu yakai 512, a cewar kwamitin dake binciken lamarin.
A baya dai an sanar da cewa mutane 358 ne suka mutu, wanda hakan ma ya zama hari mafi muni a tarihin kasar Somaliya.
Babu wata kungiya da ta ‘dauki alhakin harin. Sai dai jami’an Somaliya sun zargi kungiyar al-Qaida mai alaka da kungiyar al-Shabab da kai harin, wadda ta sha kai manyan hare-hare a babban birnin Mogadishu.
Shi dai wannan kwamiti an kafa shine domin bincikar harin na ranar 14 ga watan Oktoba a Mohadishu. Gwamtain kasar ta karbi rahotan binciken a wannan makon, amma har ya zuwa yanzu babu wata magana daga gwamnatin.
Kungiyar al-Shabab ta dade tana kokarin ganin ta hambarar da gwamnati. Inda tayi ta auna jami’an gwamnati da sojoji da fararen hula da harin bam.