Gwamnatin kasar Habasha ta ce zata rufe baki ‘daya sansanonin ‘yan gudun hijira 27 dake kasar cikin shekaru goma masu zuwa, kuma zata tsugunnar da mutanen zuwa cikin al’umma.
Kasa ‘daya ce kawai a Afirka ta fi kasar Habasha yawan ‘yan gudun hijira, a cewar hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta MDD. Sama da ‘yan gudun hijira 850,000 daga Sudan ta Kudu da Somaliya da Yamal da kuma Eritrea, ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijirar da MDD da gwamnatin Habasha ke kula da su.
A cikin watan Satumbar shekarar 2016, shugabannin kasashen Turai suka yi alkawarin samar da ayyukan yi ga ‘yan gudun hijirar kasashen Afirka na yankin sahara, da zummar rage kwararar bakin haure zuwa kasashen Turai.
An baiwa Habasha tabbacin samar mata da tallafin Dala Miliyan 500 da kuma bashi daga bakunan zuba jari na Turai, a madadin barin ‘yan gudun su yi aiki.
Facebook Forum