Mutane da dama sun salawanta yayin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da neman mutanen da abin ya shafa a cikin buraguzan bangaren gadar ta yankin Morandi da ta ruguje a lokacin a wani ruwan sama mai tsanani.
Rushewar gadar ta sa motoci da yawa sun abka da mitoci 45 zuwa kasa, yayin da gundayen kankaren simintin gadar kuma ya fada kan gine-ginen wasu ma’ajiyan kayan kamfunna dake karkashin gadar. A cewar hukumomin, dukkan wadanda suka mutun direbobin motocin dake kan gadar ne kuma babu wanda ke gefen gadar da ya mutu.
Ministan sufuri na Italiya Danilo Toninelli yau Laraba ya dora laifi a kan kamfanin dake kula da gadar ne, yana mai cewar kamfanin bata cika aikinta da kayau ba. Toninelli yace gwamnati zata kaddamar da binciken duk sauran gadojin kasar da suka tsufa hade da hanyoyin karkashin kasa da motoci ke bi a fadin kasar.